Cakwakiyar Ba Kauye

kai gaskiya a duniya indai wakar hausa kakeso kaji ta ratsa kunne, bargo da dukkanin kofofin gashin jikinka to aradun Allah ka nemi wakokin iskanci irinsu "hajiya gwale".


Wai wai wai ni fa har so nake naji anzo wurin nan da mawakin yake cewa "motarmu daban, motar gwale".

Na jima ina son na gane mai yake nufi shi wanga mawaki ashe dai, ashe dai, ashe yana nufin a gwale kunkuru ta bakin babangida mai gurmi, to amma fa kunkurun matsin cinya mai ruwa.

"Sitiyarin kan nada laushi (nono)  in baka samu ba babu haushi na na na", kaiii gaskiya namaroko bansan wanne irin duka zaici ba idan ya mutu bai tuba ba.

Ance kowa kansa yake kalla banda kallon wani, "uhmm bara nayi shiru", kar na tsunkulo wa kaina wuta.

Ni fa a rayuwa ta indai kana son kaga ina maka dariya ina shewa kawai ka kamomin daya daga cikin wakokin nan biyu zuwa uku.

Ko dai ka kamomin  ta  "Tabanan gana yarinya taba nan gana", ko kuma wakar  "babangida mai gurmi, wai daya kwana a dakin karuwa mai kai-kai (kanjamau) ai gwara na kwana a hannun 'yansanda amma fa da safe a hidda shi".

Dare yayi dare, dare marufar asiri gaba dai gaba dai "wayyo dadi, kasheni dadi" ba'a magana kawai.

Sai babban shahararren mamaki na "namaroko" mai wakar hajiya gwale, shi yasa ma nake baku labarin hajiya gwale motarmu daban motar gwale ehhhuuuhuuu.

Rankatakab kauyenmu idan ka hadesu rigif waje guda to kowa yasan da zaman "skipper na hajiya gwale".

Tun da inna ta haifanni a kauyenmu "masu gindi" ban taba yin tafiya mai nisan wacce na taba yi ba sai akan wakar hajiya gwale.

Tun daga kauyen masu gindi na fara tattaki da jakata a rataye bisa kahwaduna kamar wani bafillancen tashi har birnin kano, nan na samu nayi zango a kasuwar 'yan kaba kafin na karasa cikin birni.

Wai "tsula" aradu birni da kyau yake, kai amma fa baffa ya shusheni daya kaini can kaiye marar dadin suna waishi "masu gindi" sai kace garin kwarata.

Na tabbata yanzu haka abokai kuma biye dani, kai gaskiya zakusha labari sanka kamar soyayyen gasasshen yankakken nama "gunduwa gunduwa din kenan".

Bara muyo tariyar baya in kasheku da labari...

****
Sunana  skipper boy amma fa sai bayan na shigo birni na waye na sauya sunana zuwa skipper boy amma asalin gangariyar sunana shine "asaad".

Wani abin takaici har yau ban san menene ma'anar sunan ba, kunsan kauye sai a hankali, na saba dajin sunaye irinsu Mado, Nadabo, Kundin, Ado, Mati, Tanko, Mudi, Kwairo. To amm abin takaicin ni nawa sunan kaf karkararmu bama kauyenmu ba babu mai kamarsa.

Abinka da kauyawa wai dole asaad din ma sai da aka bata shi "asadu" ake ce min ni kuma na tsani asadun nan .

Mp3 da wayar indon kauye, kowa gara duk sunbi suna zagaya sun karade duniya.

To muma irin wadannan wayoyin sunje kauyenmu wayata ta farko itace "indon kauye", yee hahah amma fa ni kaina "indon kauyen ne".

Ehe dan wayar ta dan fini suna mai dadi ma akan wanda 'yan kauyenmu suke gayamin.

Shekara guda nayi ina taro kafin na sayeta, wakata ta farko gurmin baban gida ce, sai irinsu  wakar 'Duba by NT4'  sai "hajiya gwale".

Kullum wuni nake wayar nan a kunne, gata da kara kamar tangarahon masallacin unguwarmu.

Kullum da daddare sai nabi na dami makwabta da kida, idan na kunna wayata sai karfe ukun dare nake kashewa.

Tun makota na kawo korafi har sun hakura sun zubawa ikon Allah ido.

Kai duk inda kake neman takadari aradu skipper boy yakai, "mune cin kadangaru, kamun gafiya, bushiya ce kai mufa fara ma ci muke".

Ni nine uban gayya, "idan muna gasa jangwalagwala hehehe har wani mai ne ke diga daga jikinsu, mu ko muna lashe harshe.

Ana zaman makokin kadangaru ni ko ina jin wakar hajiya gwale, ni da guntayen manyan yarana kuma abokaina mu tashi mui ta rawa.

Kai rayuwar kauye tayi, shi yasa kuwa banajin tsoron kadangare, a'a to ni da nake fedeshi na gasa me zai ban tsoro.

Naji waka hajiya gwale na kuma ji, naji na kara, kaiiii....

Rannan dai ina zaune a dakina cikin dare ina tinani, "lokacin kowa gara dita ba caji" nan kawai naji ji gaba daya ma babu abinda nake so sai haduwa da mawakin wakar hajiya gwale.

Cikin dare na yanke shawara gobe zan nemi gafarar iyaye na shiga duniya yawon neman mawakin wakar hajiya gwale, "to fa da wannan buri na kwana".

Ina ya Allah Ina Ya Annabi?, babu.

Allah sarkin kudira da irada, gobe kamar yau ce, asubar fari na farka.

Sabida tsabar gaggawa da kyar da kyar na samu nayi sallar asuba na gaishe da inna da baffa, nan na tsugunna gabansu na fara kwararo bayani.

Ni, " na kalli baffa na sunkuyar da kai nace, baffa dama wata magana ke tafe dani".

Inna, " tayi saurin cewa, to asaad muna sauraronka, ince ko ba shashancin da ka saba zaka mana ba?".

Ni, " na gyada kai alamar ehh".

Baffa, " ya nisa yace, asaad in a saurarenka".

Ni, " nisawa nayi sannan nace, wato baffa dama so nake na nemi izininku domin zuwa birni don haduwa da masoyi na".

Inna, " ta kalleni wani shekeke tace, cabb di jaram, aradu ba idda zaka je asadu, ta fada tana hararata".

Baffa, " ya dago kai ya kalleni yace, asaad na amince da tafiyarka".

Inna, " me kace malam?, ka amince?, ni ko bada yawuna ba wallahi tallahi".

Baffa, " nan ya tsara inna, itama da amince".

Ni, " nan na nemi yafiyarsu da gafararsu suka yafemin har na dago zan koma dakina domin hada kayana sai baffa yace , 'asaad dana' na koma na tsugunna".

Yace, " kafin ka tafi ina so na jaddada maka wasu muhimman abubuwa da zaka rike a rayuwa don cin nasara".

Nace, " baffa ina saurarenka".

Yace,  " idan kana so kaje lafiya ka dawo lafiya to ina mai shawartarka daka rike abubuwan nan da zan fada maka, na farko ka zama mai gaskiya a duk inda kake, na biyu ka zama mai rikon amana, na uku ka kasance mai son zaman lafiya, na hudu ka kasance mai yawaita sallah da rikon addini, na biyar ka guji zina tana rage kima da daraja, yace a karshe ina mai maka fatan Alkahiri a rayuwa Allah ya sada fuskokinmu da alkhairi".

Nace, " ameen baffa".

Na kara dagowa zan mike inna ma tace, "dakata dana nima da tawa maganar, uhmm uwa da 'da sai Allah".

Tace, " zanso dana ka guji munarfuci da gulma, ka guji son zuciya da yardar Allah zaka je lafiya ka  dawo lafiya".

Nan baffa da inna suka rakani da addu'a, na shige daki na ratayi jakata bakko na makala sanda a kafada bakko ta na jikinsa.

Na dankwara wata tsohuwar hulata babu guga balle tamin kyau, baffa suka rakoni har kofar gida sunamin addu'a.

Na fice gidanmu da kafar dama, ayye kaga makota da jama'ar gari ma bankwana suke min.

Allahu Akbar Allah Mai Girma, yau muke gobe wasu ne, abokaina ma suka zo muka gaggaisa sukamin kyakkyawar addu'a.

Mutane nata mini bankwana har bakin gari suka rakani, nan na samu wani mai keke ya ragemin hanya muna tafiya muna tafiya har muka bacewa 'ya garinmu.

Tafiya maganin gari mai nisa, haka kuma tafiya sannu sannu kwana nesa.

Cikin ikon Allah haka mai keken nan ya wuce dani wani kauye dake wata babbar hanya bai wata wata ba kuwa ya saukeni a kan babbar hanyar ya juya ya koma kauyensu shima yana mini bankwana.

Bana da ko sisi, gashi ban fadawa baffa bani da kudi ba, nan na fara tafiya a kafata ...

Rana ta farko ina cikin tafiya na sauka a waji dan karamin gari bayan shafe awanni ina tafiya ba hutu, " shi garin kusan duka 'yan iska ne".

Kwarata sunyi yawa a garin, tsabar iskanci akan rasa wadda zai saukeni a matsayina na bako sai gidan me gari naje ya saukeni a gidansa.

Daga nan cakwakiyar mawaki skipper boy ta fara.

Karshen Cakwakiyar Bakauye Kenan Episode 1, Da Yardar Allah a sati na gaba zamu ci gaba da rubuta cakwakiyar bakauye episode 2.

Ina masoya skipper boy?, to fa ga labari ya samu kyauta kyauta bonanza bonanza.
Thanks For You Reading The Post We are very happy for you to come to our site. Our Website Domain name https://www.skipperboyblog.com.ng/.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

Comments

Post a Comment