Dan SojaNa fara rubutun littafin nan ne ranar juma'a, ashirin da shida ga watan july 2019.

                                             Friday 26th July, 2019.

____The heart touching story of gallant, legend soldier's son and his royal family members who exists to serve The Nation with all their lives_____


An haifeni ne don na kare kasata da al'ummar kasata, ni  bawan kasa ta ne " Mahaifiyata ta haifeni ne don na sadaukar da rayuwa ta don kare dukkanin al'ummar kasata, da ceto rayuwarsu daga dukkanin harin 'yan ta'adda".     

I was born to be a soldier who will serve his nation.

Sunana Amir Muhammad Abu Ali, ni uban 'yan tada kayar baya ne. kuma ni makashin maza ne " Na tabbata wata rana maza ne zasu kasheni kamar yadda suka kashe mahaifina Muhammad Abu Ali".

Ni Soja ne, dan soja, jikan soja kuma burina a rayuwa bai wuce nima na haifi 'da namiji soja ba ko kuma na haifi bataliyar soji " Makasan Maza".

Indai wannan burin nawa ya cika, kai koda 'da daya na haifa a duniya na mutu a filin daga na tabbata ban mutu a banza ba, kuma na mutu a matsayin jarumin soja ne, wanda al'umma zata masa addu'a da sa albarka kuma tayi alfahari dashi.

A tsarina babu wariyar launi fata, yare ko kuma addini gani nake 'all humans are equal', idan ina yaki 'dan ta'adda kawai nake kashewa, bana son abinda zai ke taba al'ummar kasata wadanda ni da sauran sojoji muke sadaukar da rayuwarmu saboda su.

Mutuwa karar kwana ce, ko kana gadon barcinka idan tazo sai fa mun tafi to wai saboda me ba zamu ke shiryarta ba?, ya zama kowanne lokaci muna ready.

Kowanne lokaci rayuwarmu kamar ruwa ne a cikin kofi a dorashi bisa bayan kifaffen dan koko, hakan na nufin rayuwarmu kowanne lokaci cikin tambal tambal take so mu shiryawa mutuwa kowanne lokaci hakan nada matukar amfani a rayuwar soja kai har da ta al'umma baki daya.

Ni dan asalin Jihar Kogi ne, karamar hukumar Bassa Local Government, titin da yanzu haka muke bi nida  da 'yan uwana mata  mu ziyarci asalinmu sunansa 'Shintaku-Gboloko-Dekina Road' dake karamar hukumar Bassa.

Mahaifina Muhammad Abu Ali sadaukin jarumin soja ne mai zuciyar jarumai 'da ga  Sarkin {Ettu} Masarautar Bassa-Enge, Birgediya Janar mai ritaya Abu Ali, kakana kenan wanda nake matukar so a rayuwa.

A takaice ni jini ne kuma jikan masaurautar Bassa-Enge.

Haka kuma ni 'da ne ga mamana 'Samira', jika kuma ga kakata 'Hajiya Fatima' mahaifiyar baba na muhammad abu ali.

Shekarata Ashirin da biyu yanzu haka, amma an haifeni a jihar kaduna ne, garin mahaifiyata na taso rabi a kaduna rabi a garin kakanni na saboda ina matukar son zama da kaka na yana bani labarin irin gwagwarmayar da yayi a rayuwa lokacin da yana aikin soja.

Hmm abin gwanin ban tausayi wani lokacin wani lokacin kuma gwanin ban al'ajabi, saboda yawan samun lokacin da nake ni da kakana yasa naji ni gaba daya ma ba zan iya wani aiki a rayuwata ba in ba aikin soja ba.

Kuma ni a aikin sojan ma direban tanka zan zama, haka kuma ina fatan bada rayuwa ta wajen yin aiki tukuru don ganin nafi mahaifina da kakana matsayi a aikin soja.

Dama hausawa sunce kyaun 'da ya gaji ubansa, to nima so nake na gaji uban nawa na kuma na gaji kaka na.

An haifeni ne a ranar 25 ga watan augustan shekarar 1997, nayi makarantar sakandire a nan Jihar Kaduna amma fa a Jihar Kogi nake hutun kowanne karshen zangn karatu.

Bayan na kammala sakandire ta Government Technical College Kaduna, nayi jarabawar shiga makarantar Nigerian Depence Academy dake Kaduna a shekarar 2017, cikin yardar Allah taimakon Addu'ar iyaye na samu nasarar tsunduma cikin makarantar.

Nayi shekara biyar a cikin makaranta a karshe akayi passing out dinmu, ina da mukamin laftanal na uku a matsayin jami'in sojan kasa na Najeriya.

Ina daga cikin dakarun sojoji dake bataliya ta 270 a rundunar soji.

Yanzu haka ni ma matukin tankar yaki ne, kamar yadda mahaifina yake matukin tankar yaki.

Ni soja ne, haka kuma mahaifina ma soja ne, amma bataliyarmu daban daban, zan baku labarin gwarzon mahaifina ne wanda ya rasa rayuwarsa a yakin da sukayi da masu fafutukar kafa kungiyar boko haram a jihar maiduguri.

___________________


This is just the begining of "Dan Soja", we stop here because we need support from other fans, followers, family of muhammad abu ali.

Rubutun littafin dan soja ya dakata daga nan ne sakamakon rashin samun isassun bayanai da muka rasa game da gwarzon labarin namu wato Muhammad Abu Ali, zanso na samu ci gaban bayanai akan shi jarumi  na " my hero" domin naji dadin gudanar daci gaba da rubutun labarin cikin sauki.

Mahaifinsa dai dan jihar neja ne, sarkin masarautar bassa enge, ban sani ba ko wani zai tura mana wannan labari a yadashi har yaje ya samu iyalan muhammad abu ali domin jin yadda zata kaya.

Allah muna rokonka kasa muyi kyakkyawan karshe.

Muna godiya ga dukkanin daukacin wanda ya samu damar fara karatun labarin dan soja
Thanks For You Reading The Post We are very happy for you to come to our site. Our Website Domain name https://www.skipperboyblog.com.ng/.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

1 comment