Maganin Kara Girman Nono

Sahihan magunguna bangaren matsalar zubewar nono, kankancewarsu cikim sauki dallah dallah.

Barkanmu da haduwa daku cikin sabon rubutu na akan mata kadai masu bukatar su karin girman nono ko na duwawu (mazaunai).

Sakamakon yawan korafe korafe da nake amsa daga hannun bayin Allah, 'yan uwa mata game da neman maganin karin girman nono da kuma girman mazaunai yasa yau naga ya dace na zauna nayi rubutu mai fa'ida akan yadda kowacce mace zata gyara nononta su kara girma.

Su zama ruguza ruguza dirka dika dasu kamar yayan kankana ehh mana da gaske fa.

Farko dai sunana skipper boy kuma ni namiji ne amma fa bana da aure dan ban balaga ba.

Ana yawan korafe korafe akan wannan matsalar, to amma bari na fada muku wata magana da yaya na ya fada wani lokaci muna tafiya

Skipper Boy, " Nace 'dan uwa amma esi yafi iskar bishiya dadi ko kara lafiya ko?, (na tambayeshi innocently)."

Dan uwa, " ya sauke numfashi hadi da murmushi yace,  kanina idan kana son kaji dadin zaman duniya to dole sai ka hada da abubuwa wadanda suke natural, haka kuma shi wannan iskar ta esi tana cutarda lafiyar dan adam, so kada ma ka shagala da sonta".

Ita kuwa iska wacce take daga mahaliccinmu tafi amfani da rashin cutarwa ga lafiyarmu.

***
Maganar tasa kam abin dubawa ce, to amma kunsan indai mutum stupidity yana damunsa ya kan manta wasu abubuwan da dama a rayuwa.

Kamar yadda nayi bincike kafin na fara rubutun nan na  gano wasu matsaloli dake cikin tiyatar da akewa mata don nononsu ya kara girma kuma wallahi yana fashewa a karshe (kagasi kabari ai).

Domin gujewa mutuwa da gangan ga shiga wuta da gangan, ya zama dole mu koma amfani da magungunan musulinci, to amma fa addini shine a gaba.

Haka kuma shi kansa duwawu da muke gani a bidiyo da hotunan batsa mafiya yawancinsu wallahi na jabu ne, zaka ga abu a zagaye kamar bokiti to wallahi duwawun hadin likita ne, bana Allah da annabi bane hadashi aka yi.

Fatan mai karatu ya fuskanta.

Duk macen da take so duwawunta su kara girma yadda idan tana tafiya su kadai zasu ke rawa *ihuuu* to wallahi ta lalubi maganin gargajiya ko na musulinci.

Haka kuma idan mace na fama da matsalar rashin dirka dirkan nonuwa sbd wasu dalilai kamar, shayarwa, jinya, kirar jiki ta asali, gado da sauransu to ta nemi maganin gargajiya insha Allahu zata dace.

Ganin rubutun nawa zai dauki lokaci idan nace dole sai na fara bayani akan masu bukatar kara girman nono ko dai wasu matsalolin nasa  hadi da shawarwari.

Gyaran Nono Daki Daki Cikin Hausa Da Bayani Dallah Dallah

Yanzu haka zamu yi bayani ne dallah dallah, fatan jama'a maza da mata kowa zai amfana da wannan rubutu na mr skipper boy, domin nima mafiya yawancin lokuta bincike nake na musamman kafin na gano irin wadanna abubuwa.

Ina fata mata na tare dani.

Abinda Yake Sa Nono Ya Zama Karami ko Kanana Da Kuma Yadda Za'ayi Maganin Matsalar

Wasu matan daman haka Allah madaukakin sarki ke halittar kayansa dama can nononsu yan kanana ne kamar kwallon goruba.

Wasu matan kuwa wasu dalilai ne ke jawo kankancewar nonon nasu ko zubewarsu.

Gadai dalilan

1) - Kwanciya akan nono (akansu).
2) - Saka matsattsiyar rigar nono (breziya).

Domin magance matsalar kwanciyar nono wato kina so su tsaya sai ki gwada wannan hadin.

Ki samo garin hulba da kuma ruwan dumi, sai ki kwaba hulban da ruwan dumin amma fa ki kwaba yayi kauri kada yayi ruwa.

Bayan kin kwaba kayanki sai ki samu wuri ki ajiyeshi sai da daddare.

Idan kinzo zaki kwanta sai ki nemi matsatsiyar breziya ki adanata a gefenki.

Dauko kwababben hulbanki sai ki shafe nononki baki daya sannan sai ki saka damammiyar rigar nonon nan taki kiyi kwanciyarki abinki.

Washe gari da safe sai ki tashi ki wanke nonuwanki da ruwan dumi.

Sa'annan wannan hadi mata masu aure ma zasu iya hadawa su gwada fatan Allah ya bada nasara.

Yadda Zaki Sauya Nononki Daga Kananu Znwa Manya Kamar Balo Balo

Idan har nononki kanana ne kuma kina matukar son su zama manya to baiwar Allah zaki gwada wani hadi da zamu ajiye a kasa fatan Allah ya taimaka.

To amma fa da yardar Allah zakuyi mamaki duk wadda ta gwada wannan hadin, amma fa na masu kananan nonuwa ne tun asali.

Ga Yadda ake Hadin.

Ki samo cukwui da garin alkama sai aya da kuma nonon saniya (ko madarar ) sai kuma ki samu garin hulba ko mansa.

Cukwui din da zaki samo ana bukatar yawansa ki samo kamar guda uku, sannan sai ki samo garin alkama gwangwani daya, sai aya gwangwani daya.

Sai ki hada garin alkaman nan da cukwui dinki guda uku, da kuma ayarki gwangwani daya ki saka a turmi ki dakasu har sai sun zama gari yauwa, sai ki tankade garin.

Aa ki samu nonon saniya (irin wanda matan fulani ke talla) idan kuma bakya sha sai ki samu madara ki saya koda gwangwani daya ce ita ma.

Ki rinka diban madarar nan mai gari ko cokali uku ce kina hadawa da garin da kika tankade kina rudawa kina sha kullum sau daya.

Idan kin samu nonon shanu kinga kenan babu bukatar saka ruwa a cikin hadin naki, kawai garin dakakken cukwui, aya, alkaman ki zaki diba ki zuba a ciki ki kada ki rinka sha sau daya.

Bayani kenan cikin sauki.

To amma kuma kada a manta idan zakiyi wanka ki tafasa ruwa da garin hulba a ciki saikin tabbatar ya tafasa yana zabalbala sai ki sauke kayanki.

Ki barshi yayi sanyi sannan sai ki wanke nonon naki dashi sannan kiyi wankan da zakiyi.

Haka kuma shi wannan hadin mata masu aure zasu iya haka kuma dama 'yan mata ma zasu iya.

Fatan Allah ya datar damu ya shiryar damu tafarkin tsira.

Yadda Zaki Kara Girman Nononki Da Wannan Hadin

6ter idan kina so nononki ya ciko ya zama kamar balo balo saboda tsabar cika wohoho to wallahi ki gwada hadin da zan ajiye a kasa da yardar Allah madaukakin sarki zakiyi mamaki matuka haka kuma zakiyi mana addu'a da sa albarka.

Ga Yadda Ake Hadin.

Farko dai zaki samu aya sai ki shanyata ta bushe rakayau da ita, sai ki samu garin alkama ki hada da ayarki "kinga kenan kin samu abu biyu a hannu kenan, na farko aya na biyu kuma alkama".

To sai ki samu farar shinkafa ki hada da wannan busasshiyar ayar taki da kuma alkaman nan naki.

Yauwa sai ki zubasu a ruwa lokaci guda, ki barsu su jiki sannan sai ki markadashi ko kuma ki bada inji a markado miki.

Bayan an kawo miki sai ki tace kayanki da mataci ki fidda kullinki waje guda ki aje dusar waje guda.

Sai ki samo karashen mahadin wato zuma da madara.

Sai ki samu tukunya ki dora a wuta ki juye kullinki da kika tace, ki kawo zumar nan da madara ki zuba a ciki.

A kin hada abubuwa nawa kenan a ciki?.

Ina kin hada guda biyar kenan na farko nikakken aya, alkama da busasshiyar shinkafa , madara da zuma.

Bayan kin dafa yayi kauri sai ki sauke kayanki ki samu kofi ko wani mazubin ki juyeshi.

Sai kina sha kullum sau biyu a rana.

Kada ku manta fa, muna muku bayani ne kamar a gabanku muke duk wacce take da tambaya zata iya samunmu ta dandalin sada zumunta na watsapp amma sai a karshen jawabin zamu aje numbarmu.

Wani Hadin Dake Kara Girman Nono

To fa shi kansa fa gwadawa yace ayi, shi dai baice yana aiki dari bisa dari ba, to amma yana da yakinin maganin yana da matukar amfani kuma zai taimaka, kuma a gwada shi ke maganin mai karya.

Wacece zata gwada wannan hadi ta tabbatar mana yana aiki daga baya?.

To ba tare da bata lokaci ba ga yadda hadin yake da kuma yadda ake hadashi.

Ki samu man hulba ki rinka sha sau uku a rana, to amma fa banda mai ciki.

Sannan ki rinka shafawa a kirjinka.

Haka kuma ki samu garin shinkafa, aya, alkama, gwada, hulba duk nikasu ki rinka lasarsu kina sha amma fa sai kin hada da madara

Indai kina so nononki ya kara girma ya zama zagayayye, yayi kamar balo balo ya tsaya a kirjinki ki gwada wannan hadin da yardar Allah zaki  mana addu'a.

To amma fa addu'ar shiriya muke bukata bata komai ba.

Maganin Rage Girman Nono Idan Sukayi Tula Tula Suka Zama Munana 

Kutumar Du ma du, wai wai wai Allah kafi karfin abinsa yafi karfinmu, wato ana wata fa kenan ga wata.

Wasu na neman maganin kara girman nono ya zama kamar balo balo ya tsaya a kirjinsu,  Allahu Akbar wasu kuma wallahi nonon yayi yawa har ya zama na jinya.

Ina matuka tausaya wa mai matsala irin wannan kuma zanso ki karanta wadansu yan hade hade da na binciki ko Allah zaisa mu dace.

Haka kuma su nonuwa ana so suyi girma ne, yadda zasu rinka tayarma da mijinki sha'awa, su rinka daukar hankalinsa  haka kuma yaga suna birgeshi.

To amma idan girmansu ya wuce kima, zaki dan rasa wata darajar a wajen mijij naki.

Amma ba na son na cikaku da surutai ba kai balle gindi ga yadda ake hada maganin matsalar.

Ki nemai wadannan abubuwan.

Ki nemi ganyen lemon zaki da buhuru sudaniya ki dakasu  ki rinka shafawa a nonon naki zai ragu da yardar Allah.

Amma ki rage shan madara haka kuma idan da hali da dama ki rinka soya hanta da kitsen akuya kina ci  da yardar Allah nononki zasu ragu kuma ba zasu yi tula tula ba.

Yadda Zaki Rage Kiba Da Girman Nono Cikin Sauki

Ga wata garabasar ma, idan kina da kiba kirinka shan na'a na'a, da yardar mai sama kibarki zata ragu haka kuma su kansu nonon naki zasu ragu da yardar Allah.

Kowa dai ya sani Allah shine da magani ba mutum ba, mutum bashi da magani haka kuma Allah ne mai biyawa bayinsa bukata ba mu ba.

Bayanin Rufe Wanga Rubitu

Shi komi na duniya sauki gareshi haka kuma addinin musulinci addini ne wanda yake da saukin lamari sosai da sosai.

Ku kasance da shafina kowanne lokaci domin samu da karanta abubuwa da yawa kai harma da karuwa da abubuwa da yawa a rayuwa musamman bangaren rayuwar aure da jima'i da sauransu.

Nayi bincike sai naga al'ummar haus muna fama da matsalar rashin ilimin jima'i sosai, dan haka na dauki aniyar bada tawa gudunmawar dai dai gwargwado kafin na juya zuwa wani bangaren.

Allah shi kyauta makwancinmu ya rabam da fitinar duniya, fitinar lahira da fitinar kabari .

Kowa yayi sharhi ya hada da amin, domin neman karin bayani ku samemu a dandalin sada zumunta na watsapp ga lambar nan: +2347066712486.
Thanks For You Reading The Post We are very happy for you to come to our site. Our Website Domain name https://www.skipperboyblog.com.ng/.
Newer Posts Newer Posts Older Posts Older Posts

More posts

Comments

Post a Comment