Assalamu Alaikum.

Yaya kuke?, ina mai yiwa kowa da kowa maraba da ziyartar blog dina wato skipperboyblog, yau da yardar Allah Madaukakin Sarki zanyi wani bayani ne wanda ya danganci rayuwar matasa da dama. Maza da mata.

Magana ce mai matukar muhimmanci game da yadda ake denawa ko magance matsalar fama da istimna'i ga matasa maza da maa.

Gaskiyar magana, istimna'i babbar cuta ce mai matukar hadari ga lafiya, ta bangaren daya shafi sabgogi na rayuwa data fannin addini. A addinance wato shi ainihin istimna'i bai halatta ba ga namiji baligi ko kuma mace baliga.

Yinsa dai dai yake da aikata Zina,kunga kuwa kai bada danne diyar mutane ba kai da shan guduma, gara mutum ya taimaki kansa yayiwa kansa kiyamul laili ya daina aikata hakan.

Ina da yakini da tabbacin duk talikin dake karanta wannan post nawa to lallai yasan menene istimna'i (wasa da al'aura) hakan shine istimna'i.

Shi dai istimna'i yana da illoli da yawa ga lafiyar dan adam, kafin na baku shawarwari da kuma dabarun daina yin istimna'i ga jerin kalar illolinsa nan.

> Saurin inzali
> Yawan mantuwa
> Mutuwar idanu
> Zubar gashin jiki da tsinkewarsa
> Jawo masifu ga mai yinsa
> Wanda ya mutu yana yinsa babu shi ba rahamar Allah
> Yana jawo mutum yaji baya sha'awar saduwa da mace, ko mace taji bata son saduwa da namiji
> Yana jawo rashin haihuwa
> Yana saka shagala da addini.

Akwai illoli da yawa da istimna'i ke haifarwa mai yinsa, na rantse har da girman Allah duk wanda yake fama da cutar istimna'i yana ruwa. Domin shi wata irin muguwar cuta ce mai wuyar warkewa.

Na farko yana da saukin farawa, amma akwai wuyar denawa, duk lokacin daka saba yinsa da zarar lokacin aikata shi yayi indai baka yishi ba ji zakayi kamar baka da lafiya, har wani ciwon kai ke hawa kanka.

Bayan haka,  koda mutum yayi aure, ba zai iya denashi ba muddin bai yayeshi daga rayuwarsa ba tun yana dan karami. Koda ka gama saduwa da iyalinsa hakan ba zai hana ka aikata istimna'i ba.

Ni kaina nasha wuya da matsalar istimna'i amma da taimakon abubuwa da dama na samu nasarar yageshi daga tsarin rayuwata.

Sabida haka bari na baka shawara mai matukar muhimmanci akan yadda zaka tunbuke istimna'i daga cikin rayuwarka da taimakon ubangiji.

Abubuwa da zaka rinka yinsu domin rabuwa da istimna'i.
  1. Yawaita zikiri, salati da karatun al-quran
  2. Yawaita addu'a game da cutar istimna'i da kake fama da ita
  3. Sallah akan lokaci
  4. Ka daina kadaicewa kai kadai a cikin daki
  5. Ka daina kusantar duk abinda zai tayar maka da sha'awa. Musamman fina-finan batsa
  6. Ka rage tunani akansa, ya kasance kowanne lokaci busy kake
  7. Ka daina amfani da wayarka da daddare a daki
  8. Ka kuma nemi mahaifanka su tayaka da addu'a suma.
Ya kai 'dan uwa muddin zaka rinka yawaita karatun alqur'ani mai girma, sallah akan lokaci, da daina kadaicewa a daki kai kadai ina da yakini  ubangiji (S.W.T) zai kubutar dakai daga sharrin cutar istimna'i.

Idan hakan yayi maka wuya, ka daure kayi aure. Yadda duk lokacin da sha'awa ta taso maka babu wani amfanin istimna'i sai ka sada da iyalinka.

****

A karshe ina taya dukkanin masu bibiyar blog din skipper boy fatan alkhairi a rayuwa, Allah ya shiryamu baki daya.

Kada ku manta zaku iya kasancewa dani ta facebook, twitter ko kuma instagram ko kuma watsapp idan kuka duba buttons din "STAY WITH ME" dake wannan blog.

Na gode muku kwarai da gaske.