A takaice muna yiwa kowa da barka da zuwa,  bayan haka ina godiya ga daukacin wadanda suka bata lokacinsu wajen karanta dukkanin abubuwan da nake rubutawa.

Wala'allah na nishadi, motsa sha'awa ko kuma na fadakarwa, ah ba tare da wani bata lokaci ba yanzu zan danyi bayani akan irin aiyukan da nakeyi.

A duniyar yau komai yaci gaba idan bai kara farashi ba to lallai an samu habakar zamanantuwarsa, tabbas haka shima rubutu yake, kowanne irin mutum muddin kwakwalwarsa tana aiki zai iya zama marubuci cikin sauki.

Sai dai abu mafi wahala cikin tsarin rubutu shine yadda mutum zai tafiyar da komai a saukake kuma a tsanake.

Bana da sha'awar cigaba da yin wani bayani ba tare da na kaddamar da kalar aiyukan a nakeyi ba musamman ga wadanda suke da bukata.

☑ AIYUKAN DA NAKE YI ⬇

 1. Kerawa mutum shafin yanar gizo mai kyaun gaske akan farashi mai rahusa.
 2. Taimakawa sabon marubucin yanar gizo ya fitar da dubu gomarsa ta farko daga Okadabooks.
 3. Tallatawa mutum littafinsa akan farashi mai rahusa.
 4. Taimakawa mutum wajen wallafa littafinsa na farko a Okadabooks ko kuma wani book store din.
 5. Taimakawa mutum don ganin ya fara samun kudi da shafinsa na yanar gizo akan farashi mai rahusa.
 6. Gyarawa mutum SEO na shafinsa na yanar gizo ya rinka samun traffic sosai. 
 7. Shawarwari ga ma'aurata.
 8. Shawarwari ga masu matsalar kankantar gaba, nono, kugu da sauransu.
 9. Muhimmin training akan yadda ake takalo sha'awa (wannan na maza da mata ne).
Kadan kenan daga cikin irin aiyukan da nake yi a matsayina na namiji, amma kamin nayi bayani dallah dallah akan kowanne aiki dana jero a sama, zan dan jero irin aiyukan da bana yi.

❎ AIYUKAN DA BANA YI ⬇

 1. Kawalanci "hada wani da wata". 
 2. Secret haduwa da wani ko wata, babu ruwana da haduwa da kowa.
 3. Luwadi, bana goyon bayan hakan, kuma bana so ko sha'awar mai yinsa.
 4. Bana da sha'awar taimakawa wata wajen madiganga (madigo), so 'yan mata sai a kula.
 5. Bana bayyana bayanan wani ga wasu, misali idan munyi chat na baiwa wani lambarki (bana haka) dan haka 'yan maza sai a kula.
 6. A karshe bana hada connection (shima dai sak yake da kawalanci) dan haka 'yan maza sai ku kula domin ni ba kawali bane ehe.
Um kunji aiyukan da skipper boy shi kuma suke gaba dasu, muddin mutum yana so mu zauna lafiya ni dashi muyi doguwar mu'amala to kada yayi kuskuren tambayata ina kawalanci (hada connection) ko na bashi sirrin wani ko wata, tab balle kuma luwadi da madiganga, nan da nan za fatattaki mutum.

Duk wadannan abubuwa na barranta kaina daga garesu kuma ina fatan Allah ya mini tsari dasu kai harma masoyana.

Yauwa to yanzu kuma zan fara bayani akan irin aiyukan dana lissafo ina yinsu, kowannensu zanyi fahimtaccen bayani akansa yadda kowanne mutum zai gane ya fahimta.

Abokai!!!, ni fa ba kowa bane, sunana skipper boy kuma ni ba kano ne (dan kano) baya ga haka ni hausa fulani ne. Mama na bafillaciya shi ko Papa na BaKano.

Lokacin da nake rubutun nan har wani shauki nake ji, amma bayan na kammala rubutashi wata nutsuwa ce ta musamman ta sameni har kan gadon barcina.

🌐 Kerawa Mutum Shafin Yanar Gizo Mai Kyaun Gaske - Web Design 💻

Shin ka taba jin kalmar web design?, idan baka taba ji ba to bari na maka saukakakken bayani akan web design .

Shi web design wani aiki ne wanda wasu tsiraru cikin mutane ke koyarsa musamman domin su rinka taimakawa 'yan uwansu wurin kera musu kyawawn hadaddun websites, blogs, forums da sauransu.

Ni kaina na kasance mai sha'awar kere keren shafukan yanar gizo, wannan dalili yasa na sakashi cikin jerin aiyukan da nake yi.

Hada website abu ne mai saukin gaske idan ka iyashi, amma idan baka iya ba yana  matukar cakarwa hadi da wahala.

Idan kana son cikin satin nan ka mallaki website, blog ko forum kawai ka tuntubeni, Allah zan kera maka website mai kyaun gaske akan kudi mai rahusa.

Domin mallakar website ko blog naka na farko a rayuwa, kana iya zabar daya daga cikin cart dinmu wanda zaka biya a maka aiko.

> A free Host: mafi kankanta shine mutum zai biya 11k, a cikin kudin nasa za'a siya masa domain irin wanda yake so kamar (.com.ng , .com, .net, .xyz).

> A Paid Host: shi paid host shine irinsu wordpress, joomla da sauransu, mafi kankantar budget shine 25k, domin a ciki za'a siya masa domain, hosting, kudin aiki d sauransu.

Idan ka zabi daya daga cikin wadannan zabuka guda biyu, zaka iya tuntubata domin mu sasanta asan yadda kake so shafin ya kasance da sauransu.

Kada kaji komai, domin ni yardajje ne, haka kuma ina son mutane su rinka yarda dani dalilin da yasa na tsani cuta kenan.

Idan ka gama zabinka, zaka iya tuntubata domin kaima a kera maka website ko blog naka.

Ina fatan zakaji dadin mu'amala dani ni skipper boy.

⚡ Taimakawa Sabon Marubuci Ya Fitar Da 10k Ta Farko Daga Okadabooks 📚

Babu abin mamaki ko almara cikin tsarin rubutu ta yanar gizo, idan kana son ka rinka samun kudade a asusunka duk wata ko bayani sati biyu haka, to gaskiya kana da bukatar ka zama marubuci mai cikakken lasisi.

Akwai hanyoyi da dama wadanda rubutu musamman na litattafai ko kuma na blogs ke kawo kudi, amma mutanenmu na fuskanci sun ta'allaka ne kawai akan siyan litattafan kasuwa.

Bari kuji, ba a iya litattafan zube ake samun kudi ba, a kasashen da sukaci gaba suna sayar da aiyukansu ne online.

To muma haka abubuwa suke sauyawa a kasar hausa, yau wayar android na nemn rinjayar wayoyi keypads, ita android ana kiranta ne da suna "Duniyarka a tafin hannunka".

So indai da gaske ne duniyarka a tafin hanunka take, lallai anzo lokacin da kokai zai sauya.

_ Zan iya taimaka maka a matsayinka na sabon marubuci wajen ganin ka samu dubu goma gyan gyana a asusunka na banki da rubutu_

_ Idan kana da sha'awar jonewa dani, ni zan taimaka maka, kuma babu ruwana dan kana rubuta hausa novels ne muddin rubutunka yana da ma'ana_.

Kada ka sama kanka damuwa, indai kana sa interest akan rubutun litattafai wallahi zan taimaka maka, babu ruwana macece ko namiji.

Ka lalubeni ta watsapp idan kana son kaima ka fara amsar 10k har ba adadi kowanne wata ta hanyar amfani da alkalamin rubutu.

Domin tuntubata nemeni a watsapp akan lambata kamar haka : +2347066712486.


💰 Tallatawa Mutum Littafinsa Akan Farashi Mai Rahusa 📠

Nayi damara daram domin tallatawa duk wani marubuci ko mai kasuwa kayansa akan sassaukan farashi.

Tallata haja ko wani abu yana taimakawa sosai wajen jawo hankalin sabbin kwastomomi susan da zaman hajarka, kuma su zame maka kwastomomi na kullum.

Domin tallata littafink ko hajarka

> Tallan Littafi: Naira dubu daya 1k akan kowanne littafi daya

>Tallan Haja: Naira 2k akan kowacce haja da za'a tallata maka.

Shi tallata littafi na farko zamuyi posting dinsa a facebook page namu da profile dinmu, sai muyi share dinsa a manyan facebook groups na arewa guda 100 gyan gyan.

Bayan mun yi maka tallansa  facebook, zamu dawo shafinmu na yanar gizo "skipperboyblog" daga baya kuma mu koma twitter muyi posting din littafinka daga karshe kuma sai mu koma instagram muyi update.

Kai dakata kaji har watsapp da telegram ma zamuyi share da kuma posting din littafinka.

Ga masu hajoji su zamu linka aikin da zamu yiwa mai littafi ne, idan kana so sai kayi maza maza ka tuntubeni.

A shirye nake kowanne lokaci.

👉 Tallafawa Mutum Wajen Ganin Ya Wallafa Littafinsa Na Farko a Okadabooks ko Wani Book Store Din 😎

Na daga cikin aiyukan da na bada himma sosai garesu, wato na tallafawa marubuta masu tasowa domin ganin littafinsu na farko an samu nasarar wallafashi a okadabooks.

Idan nace labari zan baku abin zai dauki dogon lokaci ne inda yin abu guda, ni da fari babu wanda ya tallafa mini don dora littafina a online book shop, amma haka nayi ta fadi tashi har nasara ta dawo hannun dama na.

Yau nayi shiri tsaf domin taimakawa wanda yake son fara publishing din books dinsa a okadabooks.

DOMIN NEMAN AGAJI KA NEMENI TA WATSAPP

💊 Taimakawa Mutum Don Ganin Ya Fara Samun Kudi Da Shafinsa Na Yanar Gizo 🌐

Me kake tunani?, haka kawai zaka rinka bata lokacinka kana ta fama da keyboard amma babu wani income?

Haba wannan ba zancen ji bane, gaskiyar magana itace babu yadda za'ayi mutum ya rinka wahalar banza.

Akwai hanyoyi da dama wadanda zaka rinka generating na income ta hanyar amfani da shafinka na yanar gizo.

Ko da google adsense, media.net, taboola, infolinks da sauran manya manyan ad networks basu karbi blog naka ba.

Ka tsaya kaji aboki, ba fa haka kawai ake ware 1 to 2 hours ana typing da keyboard ba, it's impossible dole za'a samu solution.

Ni skipper boy, zan taimakawa duk wanda yake son ya rinka samun income ta shafinsa.

Amma shi mai wannn shafin ya sani cewa, bafa haka siddan zanyi masa taimakon ba, dole sai ya bada nasha sigari.

Temako dai da gaske nake, ga wanda yake da bukata yana iya tuntubata ta watsapp domin mu zanta akan matsalolinsada maganinsu.

Naku Skipper Boy.

💧 Gyarawa Mutum SEO na Shafin Sa✔

Idan baka sani ba yana da kyau ka sani, shi traffic shine jigon kowanne blog ko website, muddi aka ce shafinka bashi da seo babu traffic gaskiyar Allah ka zama sorry.

Yana daga cikin matsalar SEO traffic din shafi yayi kasa da sauran kananan matsaloli wadanda ba kowa ne zai ganeu ba har sai ya mallaki shafi.

Nayi shiri mai kyau domin tallafawa duk wanda website dinsa ko blog dinsa yake da matsalar traffic nayi masa maganin matsalar.

Domim traffic kamar ruwa ne a jikin dan adam, idan babu ruwa komai yawan abincin da mutum zaici dolensa ya made zuwa lahira.

Haka shima traffi yake, muddin blog ko website baya samun traffi dai dai yake da matacce, sai dai mutuwar shafukan yanar gizo ta bambanta data mutane.

Mutum idan ya mutu ya mutu kenan, su kuwa websites ana iya recover dinsu bayan sun lalace ko daina aiki.

Inada yakinin zan iya gyara maka seo na shafinka ya zamana yana generating na traffic organinc one.

Domin tuntubata na tallafa maka wajen farfado da rayuwar shafinka sai ka hanzarta tuntubata ta watsapp.

Ka kula sosai, dole fa sai ka bada na sigari, indai aiki kake so a maka ehe.

😍 Shawarwari Ga Ma'aurata 💘

Au to, munzo babban gate, wannan tsarin shi kuma gaskiya yana bukatar sirri ehh.

Ba zan iya baje kolin komai da komai ba a nan dole idan mutum yana son ya amshi shawarwari ga ma'aurata to sai dai mu hade a watsapp.

Kada ka damu, wallahi sirrinka a rufe yake ruruf kamar ka kashe mutum ka birne.

Dan haka baka da wata matsala, kawai kuje watsapo domin tattaunawa akan shawarwari ga ma'aurata.

🙈 Shawarwari Ga Masu Matsalar Karamin Inji, Karamin Mazauni da Karamin Nono 💋

Choiiii, aradu kuma wannan shawarwarin naku sai dai mu hade a watsapp, nan naga akwai 'yan saido da kaka gida.

Naga aunty dina tana kallona, dan haka bari na fece daga wannan taskar sai dai mu hade  a watsapp domin kasancewa da taska ta gaba akan muhimmin training akan yadda ake takalo sha'awa🙈.

Itama maganar ba irin tamu bace ta yara, sai dai manya masu kwana suna doro suna bajewa.

If You Know You Know.

Kawai mu hadu a watsapp domin amsar taki shawarar, ko kuma taka shawarar.

Na gode matukar da karanta wannan page da kukayi

🏃 Muhimmin Training Akan Yadda Ake Takalo Sha'awa 🐒

Kunsan dan bera ma yasan kunya, uhm gashi nan shima ya dane jelarsa  a baya, hannu bisa kansa yana susar keya.

Akwai training na musamman da na shiryahi akan yadda ake takalo sha'awa, ga maigida ko matar gida.

Banda gwaurayen mata da zawarawa, amma fa wannan biya mutum zaiyi a koya masa.

Ahh to da haka ake koyon 💓 din a banza, kawai idan kana da sha'awar shiga tsarin ko kina da sha'awar shiga tsarin saiku hada wadannan requirements din.

 •  Na farko dai dole ku lalubi 1000 din da zaku biya.
 • Y Kasance kun dauko app din telegram, domin wannan kasuwar tafi karfin watsapp.
 • Kuyi rajista dashi, sai ku nemi shiga ciki domin karkade kunnuwanku da amfana.
Zabi dai ya rage ga mai shiga rijiya, idan yayi niyya sai ya shiga ta ka ko ta duwawu duk matsalarsa ce.

Wow, Alhamdulillah ina godiya ga Allah da ya bani ikon kammala rubutun nan lafiya kamar yadda na farashi lafiya.

Ina mai addu'ar Allah yasa mai karatu ya fara lafiya ya gama lafiya.

Wadannan sune kadan daga cikin aiyuka (services) din da nakeyi ga duk wanda yake da bukata.

Akwai na kyauta akwai kuma wanda mutum zai biya kudi domin ganin komai ya tafi dai dai wa daida.

Domin nemana: +2347066712486